Episodes 245
Avg. Duration 28m
Activity Highly Active
Since May 2021
Latest Episode Feb 2026

Publishing Details

Schedule
Weekly
Format
Episodic
Consistency
76%
Hosting
feeds.buzzsprout.com

About This Podcast

Shiri ne da ke tattaunawa mai zurfi a kan batutuwan da suka shafi al'umma kai-tsaye, da nazari a kan tasirin da za su iya yi, da nemo hanyar magance ko kauce wa illolin da za su iya hifarwa bayan jin ta-bakin wadanda abin ya shafa.

Explore Statistics

Recent Episodes

Takaddamar Da Ta Dabaibaye Zargin Sacewa Tare Mayar Da Walida Abdullahi Kirista

Feb 25, 2026 31m

Takaddama ta dabaibaye batun wata matashiya mai suna Walida Abdullahi, bayan iyalanta sun zargi wani jami’in Department of State Services mai suna Ifeanyi Onyewuenyi da sace ta daga gidansu tare da…

Halin Da Zawarawa Ke Tsintar Kansu A Ciki A Watan Ramadan

Feb 18, 2026 31m

Kowane Musulmi da yadda yakan shiga watan Ramadana – wani kan shiga da shiri, wani kuma da shiririta. Sai dai wasu watan kan zo musu da kalubale – ba don sun shirya mishi b aba kuma don sun gaza…

Yadda Bude Kan Iyakokin Najeriya Da Jamhuriyar Benin Da Niger Zai Amfani Alummar Kasashen

Feb 11, 2026 20m

A watan Agustan shekarar 2019, gwamnatin Najeriya ta rufe kan iyakokinta da wasu ƙasashe makwabta ciki har da Jamhuriyar Nijar da Jamhuriyar Benin. Wannan mataki a wancan lokaci an ɗauke shi ne domin…

Mene Ne Ya Fi Kawo Samu Tsakanin Sana’a Da Digiri?

Feb 04, 2026 27m

An dade ana muhawara a tsakanin masu sana’a da masu digiri, musamman wadanda suka yi gam-da-katar suka samu ayyuka masu tasiri, kan abin da ya fi kawu samu.Ko wanne bangare yana da kwararan hujjoji;…

Shin Ko Dawowar Dimokradiyya Ta Samar Da Kyakkyawan Fata Ga ‘Yan Najeriya?

Jan 21, 2026 18m

A farkon Jamhuriya ta Hudu a shekarar 1999, dawowar Najeriya mulkin dimokuraɗiyya ya haifar da babban fata a zukatan ‘yan ƙasa, inda mutane suka yi tsammanin ƙarshen mulkin soja zai kawo adalci, ci…

Yadda Tattalin Arziki Da Ababen More Rayuwa Suke A Farkon Jamhuriya Ta Hudu Da Kuma Yanzu

Jan 14, 2026 26m

A shekarar 1999, lokacin da Najeriya ta sake komawa mulkin farar hula, tattalin arzikin ƙasa da kayayyakin more rayuwa na cikin wani yanayi na dogon mulkin soja. A wancan lokaci, masana da manazarta…

Dalilan Da Suka Sa Matan Wannan Zamanin Ba Sa Son Talaka

Dec 31, 2025 26m

A da soyayya na kafuwa ne sakamakon gaskiyar mutum, ko nasabarsa, ko tarbiyyarsa ko kuma riko da addininsa.  Mace kan so saurayinta ko da kuwa ba shi da ko anini, a wasu lokutan ma ko da wani mai…

Yadda Ragin Farashin Man Fetur Zai Shafi Rayuwar ‘Yan Najeriya

Dec 17, 2025 15m

Rage farashin man fetur a Najeriya na daya daga cikin batutuwan da ke daukar hankalin al’umma, musamman ganin yadda tsadar rayuwa ta yi wa ’yan kasa katutu a ‘yan watannin nan. Man fetur ba wai kawai…

Ko Ziyarar Tawagar Amurka Za Ta Kawo Karshen Matsalar Tsaro A Najeriya?

Dec 10, 2025 13m

A kwanakin nan, tawagar ’yan majalisar dokokin Amurka ta kawo ziyara Najeriya domin tattaunawa kan tsaro da tashin hankalin da ake ta fama da shi a yankunan Arewa da tsakiyar ƙasar, musamman…

Kalubalen Dake Gaban Janar Christopher Musa A Matsayin Ministan Tsaro

Dec 03, 2025 28m

Ana sa ran Majalisar Dattawa za ta tantance tare da tabbatar da Janar Christopher Musa mai ritaya a matsayin Ministan Tsaro, bayan da Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya aike da sunansa zuwa…

Shin Ya Kamata A Biya Kudin Fansa Ga Masu Garkuwa Da Mutane?

Nov 26, 2025 22m

A cikin 'yan shekarun nan, batun garkuwa da mutane ya zama babban kalubale ga tsaro a Najeriya da wasu ƙasashen duniya. Lokacin da mutane suka fada hannun masu garkuwa, iyaye da 'yan uwa sau da yawa…

Hanyoyin Da Suka Kamata A Bi Wajen Ceto Daliban Kebbi Da Aka Sace

Nov 19, 2025 28m

Batun kubutar da ɗalibai mata da masu garkuwa da mutane suka sace na makarantar GGCSS Maga dake karamar hukumar Danko Wasagu a jihar Kebbi na daya daga cikin abubuwan da alumma suka maida hankali a…

Tasirin Da Tura Jami’an ‘Yan Sanda Kare Manyan Mutane Zai Haifar Ga Tsaron Al’umma

Nov 12, 2025 26m

A Najeriya, an saba ganin jami’an ‘yan sanda suna gadin manyan mutane ‘yan siyasa, ‘yan kasuwa, ko shugabanni maimakon su kasance a cikin al’umma suna tabbatar da tsaro ga kowa. Wannan tsarin ya…

Yadda 'Yanbindiga Ke Amfani Da Hakar Zinare Wajen Mallakar Makamai

Nov 05, 2025 28m

Kiyasi ya nuna cewa Najeriya tana asarar sama da dala biliyan 9 a duk shekara sakamakon ayyukan masu hakar ma'adinai ba bisa ka'ida ba, kuma kaso mafi tsoka shi ne fannin zinare. Rahotanni sun ce…

Dalilan Da Suka Sa PDP Ta Ki Sayarwa Sule Lamido Fom Din Takarar Shugaban Jam’iyya

Oct 29, 2025 27m

Sabuwar dambarwa ta kunno kai tsakanin wasu manyan ‘ya’yan jam’iyyar adawa ta PDP, inda ake zargin cewa rikicin ya kai ga hana tsohon gwamnan jihar Jigawa, Alhaji Sule Lamido, sayen fom ɗin takarar…

Shin Ko Jam’iyyar PDP Ta Fara Gushewa Ne?

Oct 15, 2025 27m

Yadda ‘ya’yan jamiyyar PDP ke ficewa suna komawa jam’iyya mai mulki na cigaba da nuna yadda take kara samun koma baya a siyasar Najeriya.Banda haka, rikicin cikin gida da yaki ci yaki cinyewa na…

Yadda Aka Yi Almajiri Ya Zama Mabaraci

Oct 08, 2025 29m

A zamanin nan, ana alakanta almajirai da bara – hasali ma a lokuta da dama akan yi amfani da kalmar “almajiri” idan ana nufin mabaraci.  Amma a da ba haka lamarin yake ba – almajiri baya bukatar yin…

Tasirin Bambance-bambance Tsakanin ‘Yan Najeriya Shekara 65 Da Samun ‘Yancin Kai

Oct 01, 2025 30m

Tun daga ranar 1 ga Oktoba, 1960, Najeriya ta samu ’yancin kai daga Turawan mulkin mallaka. Amma tun daga wannan lokaci, al’ummar Najeriya sun kasance cike da bambance-bambancen addini da kabila da…

Abin Da Ya Sa ’Yan Najeriya Ba Sa Cin Kifi Yadda Ya Kamata

Sep 24, 2025 27m

Duk da amfanin kifi ga lafiyar jikin mutum da kuma samar da kudin shiga masana sun ce ba a amfani da shi yadda ya kamata a Najeriya. Baya ga bai wa jiki lafiya, kifi  ka iya samar da kudaden shiga ga…

Dalilan Tashin Farashin Doya A Wasu Kasuwannin Najeriya

Sep 17, 2025 29m

A daidaikun kasuwannin Abuja da wasu manyan birane na ƙasar nan, an bayyana yadda farashin doya ke ƙara hawa fiye da yadda ake tsammani. Wannan na faruwa ne duk da cewa yanzu sabuwar doya ta fara…

Frequently Asked Questions

How many episodes does Daga Laraba have?

Daga Laraba has published 245 episodes since May 2021, covering topics in News, News Commentary.

Is Daga Laraba still active?

Daga Laraba is currently highly active with new episodes weekly. Average episode length is 28m.

Similar Podcasts